Wednesday, 22 November 2017

HASSADA MUGUN CIWO

Da sunan Allah mai rahama mai jin Qai. Salati da sallama su tabbata bisa Annabin Rahama da iyalansa da Sahabbai baki daya.
Hassada tana daga cikin mafiya girman chututtukan dake kama zuciyar 'dan Adam, ta hanashi zama lafiya da Ubangijinsa har ma da sauran mutanen dake tare dashi.
Saboda tsananin munin wannan dabi'ar ta hassada, shi yasa Allah ya umurci Annabinsa (saww) cewa ya nemi tsari daga sharrin mai hassada idan yayin da yayi hassadar.
Hassada Mazauninta shine zuciya. Shi yasa Allah yace "HAKIKA ITA ZUCIYA LALLAI MAI UMURNI CE DA MUMMUNAN ABU".
Idan mukayi nazari cikin hadisin nan wanda Manzon Allah (saww) yace : "SON DUNIYA SHINE SHUGABAN DUKKAN KUSAKURAI".
Zamu ga cewa lallai daga cikin miyagun abubuwan da Son duniya ke haddasawa acikin zuciya akwai :
- Hassada. 
- Kyashi. 
- Rowa. 
- Girman kai. 
- Yanke zumunci. Da sauran abubuwan da Manzon Allah (saww) yake hanawa.
Shi yasa Zauren Fiqhu ya rairayo wasu hadisai da kuma maganganu da nasihohi daga Manyan Magabata na kwarai domin su zama jagora garemu ko kuma madubi domin mu kauce ma kamuwa da wannan mummunan dabi'ar.
Wannan sharar fage ne. In sha Allahu gobe zamu shiga cikin fagen sosai zakuji maganganun magabata game da hassada.
Da fatan Allah shi kiyayemu ya karemu daga sharrukan fili da na boye, ya inganta halayenmu da dabi'unmu. Ameeen.
An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp -2 ranar 02-04-2017.

No comments:

Post a Comment