Tuesday 20 February 2018

LAILA MAJNUN

Laila Majnun......!!!!!!


Labari..!


Labarin soyayya ta gaskiya me cike da ban tausayi


Hikayar Laila da Majnun an ba da ita kimanin shekaru dubu da suka wuce, kuma an bayar da ita ta fuskoki da dama, to amma dukkan fuskokin sun hadu akan ginshiki daya, watau tsarkakkiyar soyayya ce tsakaninsu. Ga irin hikayar da muka rairayo:

Wani saurayi mai suna Qays ibn Mulawwah dan kabilar Banu Amar. Qays ya kasance mai fasaha da basira a makarantarsu, sai dai ya kamu da soyayyar Laila bint Mahdi Ibn Sa’ad an fi kiran ta da Laila Amiriya, a hankali ya rika nuna mata soyayya ta hanyar kulawa da sauran alamu. Duk lokacin da ta makara zuwa makaranta sai hankalinsa ya tashi ya rasa sukuni, gaba daya sai ya zuba wa kofa ido ba ya mayar da hankali ga karatunsa. Wata rana da zuciyarsa ta cika da bege, ya ji kirjinsa kamar ya fashe, bai san lokacin da ya rika rubuta sunan Laila a takardar rubutunsa ba maimakon abin da ake koya musu. Dalibai da suka ga haka sai suka hakikance lallai ya yi nisa wajen kaunar ta. Da haka ita ma Laila ta soma kaunarsa ya zamana duk makarantar an san su a matsayin masoya.

Shi Qays kamar tun yana yaro k’arami masu ilmin taurari suka bayyanawa mahaifinsa cewa zai kasance wanda rayuwarsa za ta fada cikin wahala da musiba. Suka kara da cewa idan ba a yi da gaske ba ma zai iya haukacewa. Tun daga wannan lokacin mahaifinsa ke samo masa lak’ani da magunguna da addu’oi. Yayin da ya data sai mahaifinsa ya dauke shi ya kai shi Dimashka karatu inda anan ne ya hadu da Laila.

Ita Laila ta kasance ‘yar shugaban kabilar Sharwaris, wadda a da zamanin Jahiliyya ba sa ga maciji da kabilar su Qays. Laila da Qays suka zama tamkar jini daya tsoka daya idan bai ga daya sai ya kama rashin lafiya, amma Qays abin na sa ya fi tsanani, domin kuwa har wakoki yake rubutawa masoyiyarsa yana karanta su a ko’ina. Daya daga wakokin da yayi mata ita ce:

Na so ki ya mai kyau dan gaske
Wane wata ko tauraro mai haske Kin shiga ruhina kin mammallake In babu ke to ni kuwa na hakkake Ba za ni rayu a duniyar nan ba.

A makaranta aka rinka gulmar su ana nuna Majnun duk inda ya wuce, sai ya kasance idan ka yi masa abu ka ce masa ya yi hakuri don Laila, shikenan zancen ya wuce. Da dalibai suka gano lagonsa, suka rika dauke masa kayan rubutu suna cewa ya basu domin darajar Laila. Ba musu sai ya ba su. Maubin (malamin) makarantar ya damu kwarai da irin wannan al’amari. Musamman da ya ga Qaysa wanda yanzu sunan ya bace ya koma Majnun Laila (Mahaukacin Laila) ya rubutawa iyayensu takarda yana fadakar da su halin da ‘ya’yansu ke ciki. Iyayen Laila suka cire ta daga makarantar aka kirawo wani kwararren malami yana koya mata karatu a gida. Ciwon so ba shi da magani! Maimakon hakan hakan ya yi magani sai ya dada rikita al’amari. Majnun ya daina karanta komai kullum sai kuka sai waka, duk abin da ya gani sai ya ga yana masa gizo da kamannin Laila. Nan da nan sai ya soma rera wakar so gare ta.

Mahaifin Majnun ya zo takanas ya dauke shi zuwa wajen likitoci da ‘yan tsibbu da bokaye da sauran masu da’awar magani duk abin ya zama tamkar wutar kara ana yayyafa mata fetur.

Abokai da ‘yan uwa na kusa da na nesa suka zo domin tausasa zuciyar Majnun ya daina tunanin Laila amma duk a banza. Wani daga baffaninsa ya ce masa, “wai kai Qays me ka gani a jikin Laila da ka nace mata haka? Ka zo mu je na nuna maka mata dubu wadanda suka fit a kyau da kyan fasali da asali da mulki da dukiya da sarauta ka zabi wadda ta yi maka.” Majnun ya dube shi ya girgiza kai ya ce, “idanun Majnun Qays ba wanda suke so da gani tamkar Laila.” Ya daga hannu sama ya ce, “Ya Allah! Na san ba ka yi kyakkyawa a duniyar tamkar Laila ba. Na tabbata ita tana daga asalin Hurul Aini da suka zo duniya shan iska. Ya Allah alk’awarinka bay a tashi, na tabbata daga kan Laila ba zaka sake wata kyakkyawa ba. Ya Allah ka ba ni Laila!”

Wani daga kabilarsu ya ba shi shawarar ya dauki Majnun zuwa Makka ya yi roko a ka’aba kan Allah ya dauke masa son Laila a zuciyarsa. Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . Ya k’ara da cewa, “Ko Luqman, babban malami masani na tabbata ba shi da maganin ciwon so…Idan ma yana da shi ina fata babu wanda ke tsakanina da Laila. Ya waka wadannan baitoci:

A Makka na ce da shehin malami, Wai shin wace ke cutar da ni? Shin laifi ta ke yi to a sanar da ni, Shehi ya ce “d’ana bi a hankali, Azaba na nan zuwa can gare ta
Na yi farat na ce masa “a’a na yafe, Da azaba ta samu Laila ko a gefe, Ba ni kauna gara ta same ni a lafe, Da na daina sonta a barci ko fake, Gara na mutu da ciwon kaunar ta, Sannan ya ce da murya mai raurawa, “Allah ka ba ni Laila!”


ZANCI GABA...!



1 comment:

  1. Laila Majnun - Asutechs >>>>> Download Now

    >>>>> Download Full

    Laila Majnun - Asutechs >>>>> Download LINK

    >>>>> Download Now

    Laila Majnun - Asutechs >>>>> Download Full

    >>>>> Download LINK

    ReplyDelete