Tuesday, 28 November 2017

Gidan tsohon shugaban Boko Haram zai zama gidan kayan tarihi

 


Gwamnati jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya tana son ta mayar da gidan tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, Mohammed Yusuf, gidan ajiye kayan tarihi.
Yusuf, shi ne mutumin da ya assasa kungiyar Boko Haram, amma an kashe shi a lokacin da yake hannun 'yan sanda a shekarar 2009, kuma kungiyarsa na ci gaba da kai hare-hare a jihar Borno da ma wasu jihohi a arewa maso gabashin Najeriyar.

Bulama ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa, gidan ajiye kayan tarihin zai kawo masu yawon bude ido tare da zama mai amfani ga al'ummar da ke zuwa nan gaba.
Amma mutane da dama suna fargabar cewa yin hakan zai iya raya sunan Muhammad Yusuf har abada.
Daya daga cikin masu wannan fargabar shi ne wani lauya mai fafitikar kare hakkin bil'Adama Anthony Agholahon.
Ya shaida wa BBC cewa wannan ba abu ne mai kyau ba.
"Ya kamata su yi amfani da kwalejin 'yan sandan da kungiyar ta lalata, ba wai kawai su yi amfani da gidan mutumin da ya kashe mutane ba."
Wanne suna za a bai wa gidan ajiye kayan tarihin?


Nan wani waje ne da kungiyar ta lalata a watan Fabrairun 2017Hakkin mallakar hotoFLORIAN PLAUCHEUR
Image captionKungiyar Boko Haram, wadda sunanta na ainihi shi ne Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad, ta lalata wurare da dama a Najeriya tun lokacin da ta fara ayyukanta

Kwamishinan ya bayyana wannan matakin ne a lokacin da ya halarci zaman majalisar raya al'adun gargajiya da yawon bude ido da kuma wayar da kan jama'a a garin Dutse, da ke jihar Jigawa.
Dr Bulama ya ce: "Za a sanya wa wurin suna Markaz. Muna son mu gina gidan ajiye kayan tarihi a wurin in da za a tattara bayanan dukkan abubuwan da suka faru game da yakin kungiyar Boko Haram."
Mohammed Bulama ya kara da cewa: "A lokacin da kura ta lafa, muna shirin mayar da dajin Sambisa wurin da zai ja hankalin masu yawon bude ido domin nuna wa duniya abin da ya faru a dajin Sambisa."


No comments:

Post a Comment